Wani babban jami’in kula da lafiya na kasar Birtaniya ya fada cewa cikin mutane 30 da suka sha wahala suka rika aman jini bayan sun karbi allurar rigakafin Oxford-AstraZeneca, bakwai sun mutu.
Bayyana mutuwar mutanen 7 da kasar ta Birtaniya ta yi, ta zo ne a yayin da ƙasashen Turai da yawa suka dakatar da amfani da rigakafin na AstraZeneca bayan barazanar aman jini da aka yi zargin rigakafin ta janyo.
Kungiyar Kula da Magunguna da Kulawa da Kiwon Lafiya ta Birtaniya (MHRA) a cikin wata sanarwa ta ce “Daga cikin rahotanni da suka fita na mutane 30 a 24 ga Maris, cikin baƙin ciki 7 sun mutu.”