Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ba da umarnin rufe layukan sadarwan daukacin kamfanonin waya a Jihar Zamfara.
Umarnin rufe layukan sadarwan ya fara aiki ne ranar Juma’a a wani mataki na ba wa hukumomin tsaro damar gudanar da aikinsu a Jihar Zamfara da matsalar ayyukan ’yan bindiga ta yi kamari.
Sanarwar da NCC ta fitar a ranar Juma’a ta ce, “Ci gaban matsalar tsaro a Jihar Zamfara ta ya sa ya zama wajibi a rufe layukan sadarwa gaba daya a fadin jihar daga yau Juma’a, 3 ga Satumba,
“Hakan zai ba wa hukumomin tsaron da suka dace damar yin abin da ya dace domin dawo da tsaro a jihar.
“Saboda haka ake umartar Globacom ya rufe duk cibiyoyin sadarwa a fadin jihar da wadanda ke jihohi masu makwabtaka da ita da za a iya amfani da su a cikin jihar.”
Sanarwar ta kara da cewa za a rufe layukan sadarwan ne na mako biyu a karon farko.