Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce ba zai bawa Najeriya rancen kudin da suke nema a wajen su ba matukar Shugaba Buhari bai bude iyakokin Najeriya ba.
Emmanuel Macron ya yanke wannan hukuncin ne ‘yan kwanaki kadan bayan ganawar sa da Shugaba Buhari a taron Majalisar Dinkin Duniya Na 76 da aka gudanar a can birnin New York dake kasar Amurka.
Emmanuel Macron ya ce bawa Najeriya rancen kudi kamar yadda suka nema bai da wani amfani, kuma ba zai amfanar da sauran kasashen da suke Makwabtaka da kasar ta Najeriya ba, duba ga yadda rufe iyakokin kasar ya haifarwa kasashen da suke makwabtaka da kasar karayar tattalin arziki.
Don haka Shugaban kasar ya ce matukar Gwamnatin Najeriya na son a basu bashin wasu kudade to dole ne yazamana sun bude iyakokin kasar Wanda hakan ne zai tabbatar bashin zai amfanar da kasashen da ke da makwabtaka da Najeriya Wanda akasarin su renon faransa ne.
Fassara: Daga Kabiru Ado Muhd na jaridarmikiya.com