Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari a Jami’ar Abuja, babban birnin kasar.
Wasu mazauna Jami’ar da ba sa so mu ambaci sunayensu sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar sun kutsa kai rukunin gidajen Jami’ar da ke Gwagwalada da misalin karfe daya na daren yau.
A cewar wani malami, an sace malamai guda uku da ‘ya’yansu biyu da kuma wani ma’aikacin Jami’ar.
Bayanai sun nuna cewa ‘yan bindigar sun ci karfin masu gadin Jami’ar sannan suka kutsa kai gidajen malamain suka sace su.
Kawo yanzu hukumomi ba su ce komai a kan batun ba.
Source: BBC Hausa