• About
  • Contcat Us
Saturday, June 25, 2022
Opportunities Hub Hausa
No Result
View All Result
  • Login
  • Home
  • Scholarships
  • Home
  • Scholarships
No Result
View All Result
Morning News
No Result
View All Result
Home Hausa News

Amotekun ta kama mai garkuwa da mutane Labram Ibrahim yayin da yake haukan karya a Ondo

admin by admin
November 13, 2021
in Hausa News
0
Auto Draft
0
SHARES
9
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Jihar Ondo – Jami’an tsaron Amotekun reshen jihar Ondo, sun kama wani da ake zaton mai garkuwa da mutane ne mai suna Labram Ibrahim.

Ibrahim mai shekaru 30 yana karyan hauka ne lokacin da aka kama shi, PM News ta rahoto.

READ ALSO

Npower ta fitar da sabbin ka’idodi domin zabar ‘yan zango na biyu 2 da kuma tantance su

N-Power ta fara tantance wadanda suka sami aikin ‘yan rukunin C kashi na biyu gaba da gaba

An kama shi a garejin Akure da ke garin Ondo, hedkwatar karamar hukumar Ondo ta yanma da ke jihar, bayan zargin yanayin shigarsa da tafiyarsa.

A bisa ga rahotanni, Jami’an Amotekun da ke yankin, wadanda ke ta lura da shi, sun far masa lokacin da wasu mutane ke shirin daukarsa a cikin wata bakar motar jeep.

Wani idon shaida wanda yayi ikirarin cewa shi mai talla ne a garejin, ya ce:

“Kafin kamun nasa, an lura yana ta tafiya tamkar mai tabin hankali zuwa da kuma daga garejin Akure zuwa mararrabar Itanla kafin wata bakar motar Jeep ta yi fakin a kusa da shi da nufin daukarsa.

“Yanayinsa ya haifar da zargi wanda ya sa mutanen da ke yankin suka hadu sannan suka yi masa duka.”

A halin da ake ciki, wanda ake zargin ya fallasa cewa shi ba mahaukaci bane, amma yana yi wa wani Rabiu Adamu aiki a Akure, babbar birnin jihar.

Ibrahim wanda ya yi ikirarin cewa shi dan Sokoto ne, ya bayyana cewa Rabiu, surukinsa, ya dauke shi zuwa garejin motar Akure sannan ya sanya shi a motar da za ta garin Ondo.

Ya ce:

“Mutumin ya biya direban N700 sannan daga bisani ya bani N1500 don na shiga motar da za ta je Ore sannan daga Ore zuwa Epe inda zan yi aiki. Bai fada mani irin aikin da yake so nayi ba.

“Rabiu ya zo ta baya a bakar motar Jeep dinsa tare da wasu mutane uku a ciki. Ya fada mani na cire sim dina sannan na sa shi a shataletalen garejin Akure sannan na tafi Ore kafin aka kama ni a Itanla saboda yanayin shiga na.”

Jami’an Amotekun a garin Ondo sun bayyana cewa sun shiga aiki domin kama mamallakin bakar jeep din da sauran mutane uku a Akure domin ci gaba da bincike.

Amotekun sun kama ‘yan bindiga 18 dauke da bindigogi da makamai 500 a motoci uku

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren labaran gwamnan jihar Ondo, Olabode Richard Olatunde ya saki a ranar Juma’a, 5 ga watan Nuwamba.

Taken sanarwar ita ce: ‘Da dumi-dumi: Amotekun reshen Ondo ta kama yan bindiga dauke da bindigogi da makamai 500 a cikin motocin bas uku.’

Source: Legit

Share this:

  • Twitter
  • Facebook
  • LinkedIn
  • Telegram
  • WhatsApp

Like this:

Like Loading...
Tags: Amotekun

Related Posts

N-Power ta fara tantance wadanda suka sami aikin ‘yan rukunin C kashi na biyu gaba da gaba
Hausa News

Npower ta fitar da sabbin ka’idodi domin zabar ‘yan zango na biyu 2 da kuma tantance su

June 14, 2022
N-Power ta fara tantance wadanda suka sami aikin ‘yan rukunin C kashi na biyu gaba da gaba
Hausa News

N-Power ta fara tantance wadanda suka sami aikin ‘yan rukunin C kashi na biyu gaba da gaba

June 12, 2022
Abin kunya ne ga dalibi ya kasa tara akalla N500,000 lokacin nan na yajin aikin ASUU, Malami
Hausa News

Abin kunya ne ga dalibi ya kasa tara akalla N500,000 lokacin nan na yajin aikin ASUU, Malami

June 11, 2022
Nan da makwanni kadan za a kammala aikin tura wadanda zasuci gajiyar shirin Npower Batch C2 – Sadiya Umar Farouk
Hausa News

Nan da makwanni kadan za a kammala aikin tura wadanda zasuci gajiyar shirin Npower Batch C2 – Sadiya Umar Farouk

June 9, 2022
Ganduje ya sauya sunan KUST Wudil zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Dangote
Hausa News

Ganduje ya sauya sunan KUST Wudil zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Dangote

May 29, 2022
Ana Dab Da Fara Kurɓar DATA Kyauta A Najeriya – NCC
Hausa News

Ana Dab Da Fara Kurɓar DATA Kyauta A Najeriya – NCC

May 29, 2022
Next Post
Auto Draft

Takaitaccen bayanin rayuwa, silar arzikin manya-manyan Attajiran nahiyar Afrika

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

POPULAR NEWS

Apply: Gwamnatin Tarayya Ta Sake Buɗe Shafin Cike Tallafi Mai Taken”Presidential youth Empowerment Scheme (P-YES)”

Apply: Gwamnatin Tarayya Ta Sake Buɗe Shafin Cike Tallafi Mai Taken”Presidential youth Empowerment Scheme (P-YES)”

April 1, 2022
Apply: Kamfanin Cemen Na BUA Zai Bawa Graduates Horo Na Musamman Domin Tallafawa Rayuwarsu

Apply: Kamfanin Cemen Na BUA Zai Bawa Graduates Horo Na Musamman Domin Tallafawa Rayuwarsu

December 24, 2021
An Fara Approve Na Sabon Tsarin Rancen Kuɗi Marar Ruwa Wato “Tcf Covid19 Non Interest Loan.

Tallafin Covid-19 in kaga an turo maka wannan sakon to kana cikin wadanda za’a biya

September 22, 2021
Yadda Sojoji Suka Ragargaji Turji Da Yaransa A Sakkwato

Yadda Sojoji Suka Ragargaji Turji Da Yaransa A Sakkwato

December 17, 2021
Yadda Zakayi Rijistar Kasuwancinka Da Hukumar Kula Da Kasuwanci Ta Kasa (CAC).

Yadda Zakayi Rijistar Kasuwancinka Da Hukumar Kula Da Kasuwanci Ta Kasa (CAC).

February 28, 2022

EDITOR'S PICK

Albishir Ga Matasa Maza Da Mata, Game da shirin Nigeria Youth Investment Fund 2020.

Albishir Ga Matasa Maza Da Mata, Game da shirin Nigeria Youth Investment Fund 2020.

October 26, 2020
Buhari Bai Taba Alkawarin Mayar Da Naira Daya Daidai Da Dala Daya Ba – Fadar Shugaban Kasa.

Buhari ya bada sanarwar fadada shirin N-Power domin ‘Ya ‘yan Talakawa su amfana

May 3, 2021
Zamu bawa ‘yan Nageriya mutun 98,000 bashin dubu hamisin N50,000 zuwa dubu dari uku uku N300,000 -Inji Ministar Jin Kai Sadiya Farouq.

Zamu bawa ‘yan Nageriya mutun 98,000 bashin dubu hamisin N50,000 zuwa dubu dari uku uku N300,000 -Inji Ministar Jin Kai Sadiya Farouq.

April 6, 2022
Buhari zai taimaka wa Sudan ta Kudu a yaƙi da ‘yan bindiga

Buhari zai taimaka wa Sudan ta Kudu a yaƙi da ‘yan bindiga

May 13, 2022
Opportunities Hub Hausa

OHUB HQ, No, 6 Nun Street, Off Danube Crescent, Maitama, Abuja.

OHUB Eco-System

  • OHUB SMEs Market
  • OHUB Jobs Portal

Follow Us

No Result
View All Result
  • Homepages
    • Home Page 1
    • Home Page 2
  • News
  • Politics
  • National
  • Business
  • World
  • Entertainment
  • Fashion
  • Food
  • Health
  • Lifestyle
  • Opinion
  • Science
  • Tech
  • Travel

OHUB HQ, No, 6 Nun Street, Off Danube Crescent, Maitama, Abuja.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Create New Account!

Fill the forms below to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d bloggers like this: