• About
  • Contcat Us
Sunday, May 22, 2022
Opportunities Hub Hausa
No Result
View All Result
  • Login
  • Home
  • Scholarships
  • Home
  • Scholarships
No Result
View All Result
Morning News
No Result
View All Result
Home hausa

Ramadan: Yin Azumi A Kai A Kai Na Maganin Ciwon Suga – Likita

admin by admin
April 1, 2022
in hausa, Hausa News, News
0
Ramadan
0
SHARES
37
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter
Wani kwararren likita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, Dokta Sufyan Ibrahim, ya ce yin azumi a kai a kai na daya daga cikin sahihan hanyoyin magance Ciwon Suga nau’in type-2.

Ya kuma ce yin azumin na taimaka wa masu fama da cutar rage mummunar kiba da kuma sauran sinadaran da jiki ba ya bukata.

  • Mutanen gari sun kashe dan bindiga a Kaduna
  • Gombe da Kano sun yi nasara a musabakar Alkur’ani a Abuja

Likitan wanda ke jawabi yayin wata lakcar watan Azumin Ramadan da Kungiyar Likitoci Musulmai ta Najeriya (IMAN) ta shirya a Zariya ranar Juma’a, ya kuma bayyana azumin wata Ramadan da Musulmai ke yi a matsayin lokacin kara lafiya.

READ ALSO

Babu ranar janye yajin aikin ƙungiyar ASUU’

Ganduje ya ƙwato ɗan majalisa da Ciyaman da ga hannun NNPP

Ya kuma ce azumin na taimaka wa jiki wajen kone dukkan sinadaran da ba ya bukata, ta yadda garkuwar jikin dan Adam za ta samu daidaito da karin kuzari cikin ’yan sa’o’i da fara azumin.

Kwararren likitan ya kuma lura cewa azumi na taimaka wa kwayoyin halitta su yi aikinsu yadda ya kamata a jikin mai yin ibadar.

“Kazalika, yin azumi na rage fitowar wani kari a jikin mutum lokacin da ya fara tsufa, kuma yana dakushe cututtuka da dama,” inji shi.

Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban kungiyar ta IMAN, Malam Abdul’Aziz Hassan, ya ce su kan shirya lakcar ce a kowacce shekara da nufin wayar da kan mutane, musamman mambobinsu kan muhimmanci da kuma amfanin azumin Ramadan ga dukkan Musulmai.

Ya kuma ce kungiyar na da shirin ziyartar masu karamin karfi da marayu domin tallafa musu a cikin watan.

Share this:

  • Twitter
  • Facebook
  • LinkedIn
  • Telegram
  • WhatsApp

Like this:

Like Loading...
Tags: HausaHausa NewsRamadan

Related Posts

Babu ranar janye yajin aikin ƙungiyar ASUU’
Hausa News

Babu ranar janye yajin aikin ƙungiyar ASUU’

May 16, 2022
Ganduje ya ƙwato ɗan majalisa da Ciyaman da ga hannun NNPP
Hausa News

Ganduje ya ƙwato ɗan majalisa da Ciyaman da ga hannun NNPP

May 16, 2022
LABARAIAbduljabbar ya kori lauyoyinsa
Hausa News

LABARAIAbduljabbar ya kori lauyoyinsa

May 15, 2022
Yanzu yanzu mun samu labarin cewa Ranar litinin 16 /5/2022shekarau zai tabbatar da komawar sa jam.iyar NNPP
hausa

Yanzu yanzu mun samu labarin cewa Ranar litinin 16 /5/2022shekarau zai tabbatar da komawar sa jam.iyar NNPP

May 15, 2022
Buhari zai taimaka wa Sudan ta Kudu a yaƙi da ‘yan bindiga
Hausa News

Buhari zai taimaka wa Sudan ta Kudu a yaƙi da ‘yan bindiga

May 13, 2022
An Ƙaddamar da Shirin Ƙwararrun Matasan Kasuwanci Mai Taken” Youth of Enterprise (YOE) Internship Programme Launch” Duba Yadda Zaku Cike
Hausa News

An Ƙaddamar da Shirin Ƙwararrun Matasan Kasuwanci Mai Taken” Youth of Enterprise (YOE) Internship Programme Launch” Duba Yadda Zaku Cike

May 13, 2022
Next Post
ASUP

ASUP Threatenes To Shut Down All Polytechnics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

POPULAR NEWS

Apply: Gwamnatin Tarayya Ta Sake Buɗe Shafin Cike Tallafi Mai Taken”Presidential youth Empowerment Scheme (P-YES)”

Apply: Gwamnatin Tarayya Ta Sake Buɗe Shafin Cike Tallafi Mai Taken”Presidential youth Empowerment Scheme (P-YES)”

April 1, 2022
Apply: Kamfanin Cemen Na BUA Zai Bawa Graduates Horo Na Musamman Domin Tallafawa Rayuwarsu

Apply: Kamfanin Cemen Na BUA Zai Bawa Graduates Horo Na Musamman Domin Tallafawa Rayuwarsu

December 24, 2021
An Fara Approve Na Sabon Tsarin Rancen Kuɗi Marar Ruwa Wato “Tcf Covid19 Non Interest Loan.

Tallafin Covid-19 in kaga an turo maka wannan sakon to kana cikin wadanda za’a biya

September 22, 2021
Yadda Sojoji Suka Ragargaji Turji Da Yaransa A Sakkwato

Yadda Sojoji Suka Ragargaji Turji Da Yaransa A Sakkwato

December 17, 2021
Yadda Zakayi Rijistar Kasuwancinka Da Hukumar Kula Da Kasuwanci Ta Kasa (CAC).

Yadda Zakayi Rijistar Kasuwancinka Da Hukumar Kula Da Kasuwanci Ta Kasa (CAC).

February 28, 2022

EDITOR'S PICK

Yadda Zaka Sami PTA da BTA, CBN loan cikin Sauki

Yadda Zaka Sami PTA da BTA, CBN loan cikin Sauki

December 12, 2021
Cin Hancin Milyan Ashirin N20m masarautar Kano ta bani domin na daina binciken badakalar filayen. -Inji Muhuyi Magaji

Cin Hancin Milyan Ashirin N20m masarautar Kano ta bani domin na daina binciken badakalar filayen. -Inji Muhuyi Magaji

April 16, 2021
NYIF: Kafin Jiran Training and Kuma Approval Shin NYIF Sun Tura Maka Wannan Sako?

NYIF: Kafin Jiran Training and Kuma Approval Shin NYIF Sun Tura Maka Wannan Sako?

August 3, 2021
Bankin Zenith ya kaddamar da sabon jadawalin bude account ta Whatapp

Bankin Zenith ya kaddamar da sabon jadawalin bude account ta Whatapp

December 26, 2021
Opportunities Hub Hausa

OHUB HQ, No, 6 Nun Street, Off Danube Crescent, Maitama, Abuja.

OHUB Eco-System

  • OHUB SMEs Market
  • OHUB Jobs Portal

Follow Us

No Result
View All Result
  • Homepages
    • Home Page 1
    • Home Page 2
  • News
  • Politics
  • National
  • Business
  • World
  • Entertainment
  • Fashion
  • Food
  • Health
  • Lifestyle
  • Opinion
  • Science
  • Tech
  • Travel

OHUB HQ, No, 6 Nun Street, Off Danube Crescent, Maitama, Abuja.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Create New Account!

Fill the forms below to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
%d bloggers like this: