Gwamnatin Tarayya a ranar Laraba ta sanar da cewa ta shirya tsaf domin fara shirin (GEEP 2.0) a dukkanin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.
An bayyana waɗanda za su amfana da shirin
Ta bayyana cewa a ƙarƙashin shirin, manoma 98,000 da masu ƙananan sana’o’i za su samu bashin kuɗaɗen da ba ruwa a ciki daga N50,000 zuwa N300,000. Hakan na nufin gwamnatin tarayya za ta bayar da bashin N5bn a cikin shirin. Jaridar Punch ta rahoto.
Ministan jinƙai da walwala, Sadiya Farouq, ita ce ta bayyana hakan ta hannun mai taimaka mata Nneka Anibeze, a wata sanarwa a birnin tarayya Abuja.
Hakan ya biyo bayan kammala tantance kashin farko na waɗanda su ka cancanci amfanuwa da ƙananan basussuka daga N50,000 zuwa N300,000,” a cewar sanarwar

Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya ƙaddamar da shirin, ya ce shirin zai gudana ne na tsawon shekaru 3 sannan za a rarraba kuɗaɗen ne a tsakanin jihohin ƙasar.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Gwamnatin shugaba Buhari ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna NG-CARES da naira tiriliyan 311.2 domin farfaɗo da tattalin arzikin kasa
Shirin zai bayar da ƙarfi ne wajen samar da ayyukan yi da tallafa wa masu ƙananun sana’o’i da kuma ɓangaren noma