Rahotonni daga jihar kano na Cewa A jiya ranar Juma’a 6 ga Mayun da muke ciki ne Mambobin Majalisar dokokin jihar Kano na jami’iyyar PDP 10 suka sauya sheka zuwa jam’iyar NNPP ta kwankwaso mai alamar kayan marmari.
Sulaiman Yusuf Babangida Dawo-Dawo wai wakiltar Gwale shima ya bi sahun mambobin da suka sanar da ficewarsu.
Jumulla Mambobi 10 da suka sauya shekarar daga PDP zuwa NNPP sun hada da…
- Hon Aminu Sa’adu Ungogo daga Ungogo.
- Hon Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa Dala.
- Hon. Tukur Muhd Fagge.
- Hon.Mu’azzam El-Yakub, Dawakin Kudu.
7..Hon. Garba Shehu Fammar Kubiya.
- Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki, Kumbotso.
10- Hon Sulaiman Babangida Dawo-Dawo, Gwale.
Sanarwar hakan na zuwa ne bayan da Daraktan yada labarai na majalisar Uba Abdullahi ya fitar kuma aka rabawa manama labarai a makon daya gabata.
A gefe guda Kuma an Hango Hon Tijjani Abdulqadir Jobe Dan Majalisar tarayya Mai wakiltar Rimin Gado, Tofa da dawakin tofa a gidan Sanata Rabi’u Musa wanda ake Zargin ya Koma jam’iyar NNPP sakamakon Rashin nasarar da suka samu a kotun koli jiya a rikincin da suke da Gwamnan jihar kano kan batun Shugabancin jam’iya.
Jam’iyar NNPP ta kwankwaso na cigaba da samun karbuwa ga jama’a musamman a arewacin nageriya.