Jami’ar Al-Qalam da ke jihar Katsina ta ce hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa watau NUC, ta ba ta izinin gudanar da ƙarin kwasa-kwasai 13 a jami’ar.
Kakakin Jami’ar, Akilu Abubakar, shi ne ya bayyana haka a ranar Asabar ɗin da ta gabata a Katsina.
Katsina Post ta tattaro cewa, NUC ta jaddada amincewarta ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 9 ga Watan Maris da kuma aiko ma mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Nasiru Musa-Yauri da takardar.
Wasiƙar daina ɗauke da sa hannun mataimakin darakta mai kula da harkokin NUC, Mista SS Ikani a madadin babban sakataren NUC, Farfesa Abubakar Rasheed.
Shugaban yace, jami’ar Al-Qalam ta taka rawar gani a aikin bada izinin tantancewa daga NUC a tsakanin watan Nuwamba da Disamba a shekarar 2022.
A bisa ƙa’idojin da aka amince da su, ƙungiyoyin NUC sun tantance ƙarin karatun digiri a kwasa-kwasai 13 na jami’ar da suka bazu tsakanin Kwalejojin Kimiyyar zamantakewa da Gudanarwa, Kimiyyar Kwamfuta da Kimiyyar Yaɗa Labarai, Ilimi da Kimiyyar Halitta da Aiyuka, da sauran su.