Jami’ar FUDMA Dake Katsina Ta ɗaga ɗarajar Malamai 8 Zuwa Farfesoshi

Majalisar gudanarwa ta Jami’ar Tarayya dake Dutsin-Ma (FUDMA) a jihar Katsina, ta amince da ƙarin girma ga ma’aikatan Ilimi guda takwas zuwa matakin Farfesoshi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa daga hannun kakakin jami’ar, Malam Habib Umar-Amin, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Yace ƙarin girma ya biyo bayan nasarar dawowar tantancewar da suka samu a wajen, tare da ƙwazon su da sadaukarwar su ga aikin su.

Katsina Post ta samu cewa, Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Armaya’u Hamisu-Bichi ne ya sanar da hakan a yayin taron majalisar Dattijai karo na 105 na cibiyar.

Hamisu-Bichi, wanda shi ne mataimakin shugabar jami’ar, ya taya ma’aikatan da aka ƙara musu girma

murna, sannan ya buƙace su da su ƙara himma wajen ciyar da harkokin koyarwa da koyo da bincike da kuma hidimar al’umma.

A yayin sanarwar, ya lissafo waɗanda aka ɗaya darajar su zuwa Farfesoshi, waɗanda suka haɗa da; Dr Aliyu Umar na Sashen Kimiyyar Halittu wanda a yanzu Farfesa ne a fannin Parasitology da Kiwon Lafiyar Jama’a, da kuma Dokta Yahaya Mohammed na Sashen Kimiyyar Dabbobi, wanda a yanzu Farfesa ne a fannin ilimin halittar dabbobi da Dr. Muhammad Ghazali-Garba na Sashen Kimiyyar Dabbobi, Dakta Aliyu Ibrahim-Kankara, Sashen Kimiyyar Kasa, da kuma Dokta Badaki Olusegun-Lasisi, Sashen Kinetics da Ilimin Lafiya.

Sauran sun haɗa da; Dr Ahmad Muhammad-Gusau, Sashen Nazarin Addinin Musulunci, Dokta Muntaka Mamman, Faɗaɗa Noma da Raya Karkara da Dr Florence Nwamaka-Ikechiamaka daga Sashen Physics.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *