
Jami’ar FUDMA Dake Katsina Ta ɗaga ɗarajar Malamai 8 Zuwa Farfesoshi
Majalisar gudanarwa ta Jami’ar Tarayya dake Dutsin-Ma (FUDMA) a jihar Katsina, ta amince da ƙarin girma ga ma’aikatan Ilimi guda takwas zuwa matakin Farfesoshi. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa daga hannun kakakin jami’ar, Malam Habib Umar-Amin, a ranar Juma’ar da ta gabata. Yace ƙarin girma ya biyo bayan nasarar dawowar tantancewar da…